Poem in Hausa
Tsoho da dila
Tsoho ya zana layi a rairayi sannan ya ce:
"Mai yiwuwa ba za ka iya ƙetare wannan layi ba."
Sannan ya zana da’ira yana cewa:
"Dole ka tsaya a cikin wannan da’irar.
Za ka iya ƙetare ta, amma ba ta kan layin ba".
Sannan sai hadari ya zo sai layin ya ɓace.
Dila yana nan dai tsaye a cikin da’irar.
Sanyi da ruwa ya masa duka, amma bai matsa ba.
Bai sani ba ko wannan layin yana nan har yanzu,
a yayin da kuma zanen ya ɓace a kan rairayi.
Translated into Hausa by Jibril Shu'aibu Adamu